Yau alhamis Sashen Hausa na Muryar Amurka yake shirin gudanar da taron yaki da cutar kwalara da wasu cututtukan dake addbar mata da yara kanana a hotel na Zaranda dake Bauchi a yankin arewa maso gabashin Najeriya.
Za a fara gudanar da wannan taron da karfe 2 na azahar.
Kwararru a fannin kiwon lafiya, cikinsu har da Dr. Musa Mohammed Dambam, shugaban hukumar tsara kula da lafiya tun daga tushe ta Jihar Bauchi, da Dr. Habib Sadauka na kungiyar T-Ship, da kuma Louise Daniel, kwararriya kan cututtuka masu yaduwa, zasu gabatar da kasidu kan wadannan cututtuka.
Haka kuma, kwararrun 'yan wasan kwaikwayo na ban dariya na Hausa Ibrahim Isah Yado (Ibron Kaduna), Mahmud Shashasha, da Umar Sususu da Aisha Motar Kara da wasunsu zasu gabatar da wasanni kan wadannan cututtukan.
Hukumar Tallafawa Kasashe Masu Tasowa ta Amurka, USAID, ita ma ta turo wakilanta da kwararru a fannoni dabam-dabam domin jin wadannan kasidu tare da nazarin hanayoyin da zata iya kara tallafawa.
Jihar Bauchi na daya daga cikin jihohin da annobar cutar kwalara ta fi yi wa illa a wannan shekara.