Shugaban Faransa, Francois Hollande ya yi kira ga bangarorin biyu da su zabi makoma ta zaman lafiya yayin da ya ke bude taron.
Ya kara da cewa dole ne Isra’ila da Palasdin su saka tunanin zaman lafiyan yankin a zukatansu, a maimakon burin kansu.
Hollande ya kara da cewa kasashen duniya na da muhimmiyar rawar da za su taka, amma ya rage ne ga Isra’ila da Palasdinu su yi dubi kan takaddamar da ke tsakaninsu.
Wani jami’in Amurka ya ce taron da ake yi a Paris, ba da nufin cusa wani ra’ayi ne ga bangarorin biyu ba, hasali ma Amurka kofarta a bude ta ke na karbar shawarwai kan yadda za a sulhunta Isra’ila da Palasdinu.