Yayinda yake jawabi bayan an tashi daga taron shugaban kungiyar gwamnonin gwamna Kashim Shettima na jihar Borno yace wajibi ne al'ummar arewacin Najeriya su rungumi hakurin zama da juna.
Inji gwamna Shettima sun tattauna a taron kuma sun cimma daukan wasu matakan hadin kai da zaman lafiya da juna a matsayin kasancewa 'yan arewa. Yace ko sun so ko sun ki dole ne suyi hakuri da juna, su rungumi juna, su tallafawa juna da zummar zama tare.
Gwamnonin sun tabo batun rikici tsakanin Fulani da manoma a yankin arewacin Najeriya. Kungiyar ta kara da cewa wadanda suke haddasa fada bakin haure ne dake haurowa daga wasu kasashen dake makwaftaka da Najeriya.
Kungiyar ta baiwa gwamnatin tarayya shawara a dauki mataki.Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje yayi karin haske. Yace babu shakka akwai Fulani da yawa da suke shigowa daga Afirka ta Yamma da shanu da yawa wadanda suke haddasa rikici. Sun kira gwamnatin tarayya ta tabbatar da tsaron iyakokin kasar domin a yiwa duk wadanda suke shigowa rajista..
Su gwamnonin arewan sun kuduri aniyyar canza rayuwar Fulani ta yadda suke kiwon shanu, domin a yi kiwo irin na zamani.
Shi kuwa gwamnan Kaduna Nasiru El-Rufai, jihar da tayi fama da rikicin Fulani da 'yan kudancin jihar ya nuna godiya ga gwamnonin bisa shawarwarin da suka bayar akan shawo matsalar jihar.
Ga rahoton Isa Lawal Ikara da karin bayani.