Yace su cigaba da sa ido domin gano 'yan kungiyar Boko Haram dake cikinsu domin a zakulosu.
Duk da cewa sojoji na daukan matakai daban daban na tabbatar da tsaro a kasar amma sojoji kadai ba zasu iya kammala aikin ba balantana a tabbatar da cikakken tsaro. Wajibi ne jama'a su taimaka tare da sa ido da kiyayewa.
Janar Rabe Abubakar yace idan suna sa ido sosai to duk wanda suka gani basu yadda dashi ba walau basu sanshi ba ko kuma yana wani labe-labe su sanarda hukuma. Jama'a su sani cewa 'yan ta'adan sun bazu kuma suna iya yin la'ani amma da kyar su sake taruwa wuri guda sai dai idan an yi sakaci.
Suna bin masallaci har a kasar Kamaru suna barna amma da yaddar Allah sai an ga bayansu, inji Janar Abubakar.
Wannan lokacin ya kamata a dinga bincike a masallatai da mijamiu da kasuwanni domin kada a bari su cigaba da yin barna. Jama'a su sani 'yan ta'ada na anfani da dabaru iri iri.
Ga rahoton Umar Faruk Musa da karin bayani.