'Yan bindigan da suka addabi jihar Neja basu mika makamansu ba kamar yadda sojoji suka gargadesu suyi, yanzu sai a jira a ga matakan da sojojin zasu dauka nan gaba.
Baicin kin mika makamai ana samun ayyukan ta'adanci a yankin arewacin jihar ta Neja da suka hada da sace mutane da shanu.
Alhaji Huseni Boso mataimakin shugaban kungiyar Fulani ko Miyetti Allah ta kasa yace mutanensu Fulani sun fi shan bakar wahala a yankin. Yace suna da labarai iri-iri na sace mutane tare da wawure dabbobinsu. Yace abun mamaki babu wanda ya taba 'yan bindigan duk da cewa hakkin gwamnati ne ta kare rayukan jama'a da dukiyoyinsu.
Tun bayan taronsu na makon jiya ana cigaba da satar mutane kuma ko "jiya an sace mutane biyar" inji Alhaji Boso. Yace Allah kadai ya san iyakan mutanen dake hannun bata garin a daji, dajin da inji Alhaji Boso bai wuce abun da hukumomin tsaro zasu shiga ba su gama da 'yan ta'adan.
Shugaban karamar hukumar Rafi dake fama da matsalar, Gambo Tanko Kagara yace ko a wannan makon 'yan bindiga sun yi awan gaba da wasu 'yan mata biyu kana suka buga wa mahaifinsu ya biyasu nera miliyan bakwai. Ya gaya masu bashi da miliyan bakwai amma su cigaba da rike 'yan matan su dauki nauyinsu.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari da karin bayani.