Sarkin Musulmi yayi jawabin ne a wurin taron gwamnoni da sarakunan arewa da aka gudanar a garin Kaduna.
Yace mun damu da yadda ake anfani da wuraren ibada ana wa'azin tada hankali da cusa akidar kiyayya da kyama da kuma maida hankali akan abubuwan da ka raba kawunan mutane maimakon fadin abun da zai kawo hadin kai a matsayin mutanen da Allah daya ya halircesu.
Taron gwamnonin arewa goma sha tara da sarakunan gargajiya an shiryashi ne a garin Kaduna da nufin neman mafita ga al'ummar arewa, musamman tashe-tashen hankulan da ake fama dasu a wasu jihohi cikinsu har da jihar Kaduna.
Wasu malaman addini na cigaba da warware duk wani kokarin dinke baraka tsakanin al'ummomin arewa kamar irin kalamun da Pastor Johnson Suleiman yayi inda ya kira mabiyansa su kashe duk Dan Fulanin da suka ga ya shigo farfajiyar mijami'arshi.
To saidai tuni wasu malaman addinin Kirista suka ce kiran daukan matakin fansa ya sabawa koyaswar addinin Kirista. Rabaran James Hayab daya daga cikin manyan malaman addinin Kirista a jihar Kaduna yace Bible bai koyas da daukan fansa ba. Yace malamin da yayi maganar daukan fansa maganar kansa yayi ba ta Allah ba.
Ita ma kungiyar Kiristoci ta Najeriya CAN reshen jihar Kaduna ta nuna damuwa game da wa'azin daukar fansa. Sakataren kungiyar Rabaran Sunday Ibrahim yace idan yace ya dauki fansa to ke nan ba za'a kare rikicin ba. Yace abun da ya faru ya riga ya faru saboda haka domin Allah kowa ya kwantar da hankalinshi a zauna a nemi wadanda suke tada yamutsi a hukumtasu ta haka za'a shawo kan lamarin.
Su ma shugabannin addinin Musulunci sun ce bai dace a dinga koyas da mabiya su dinga daukan matakin fansa ba. Shaikh Haliru Maraya malamin addinin Musulunci a jihar Kaduna yace addini bai yadda wani ya dauki doka a hannunsa ba, haka ma dokar kasa bata yadda ba.
Kazalika kungiyar Fulani ta Miyetti Allah reshen jihar Kaduna ta musanta rade-radin shirin daukan fansa.
Ga rahoton Isa Lawal Ikara da karin bayani.