Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tarin Fuka Na Iya Kashe Mutane Miliyan 10 Nan Da Shekaru Hudu


Wata mace mai suna Pinky Molefe, tana karbar maganin tarin fuka ko TB a wani asibitin unguwar Alexandria a Johannesburg, Afirka ta Kudu ranar 13 Oktoba, 2010
Wata mace mai suna Pinky Molefe, tana karbar maganin tarin fuka ko TB a wani asibitin unguwar Alexandria a Johannesburg, Afirka ta Kudu ranar 13 Oktoba, 2010

Tarayyar Kungiyoyin agajin Red Cross da Red Crescent ta Duniya tana neman dala miliyan 250 domin tallafawa masu fama da tarin Fuka na TB a duniya

Tarayyar Kungiyoyin agajin Red Cross da Red Crescent ta Duniya ta yi gargadin cewa mutane miliyan 10 ne zasu iya mutuwa a duniya nan da shekaru hudu masu zuwa a sanadin cutar tarin fuka ko TB.

A cikin rahoton da ta bayar jiya alhamis, ranar Cutar Tarin Fuka ta Duniya, gamayyar kungiyoyin agajin ta ce tana kokarin samo dala miliyan 250 domin taimakawa mutane miliyan daya da dubu 700 masu fama da cutar tarin fuka su samu jinya da kuma tallafi. Amma kuma tarayyar kungiyoyin agajin ta ce a zahiri ana bukatar dala miliyan dubu 21 ne domin takalar wannan annoba ta tarin fuka a duniya.

Tarin Fuka Na Iya Kashe Mutane Miliyan 10 Nan Da Shekaru Hudu
Tarin Fuka Na Iya Kashe Mutane Miliyan 10 Nan Da Shekaru Hudu

Wata kwayar halittar cuta wadda ke kama huhu, ita ce take haddasa tarin fuka ko TB. Idan har aka kama da wuri, ana iya warkar da wannan cuta da kwayoyin kashe cuta. Haka kuma ana iya yin rigakafinta da allurar rigakafi. Amma duk da haka, miliyoyin mutane su na kamuwa da tarin fuka su na kuma mutuwa a kowace shekara, akasari a kasashen Afirka da Asiya.

Kuma a saboda wasu masu fama da cutar ta tarin fuka ba su kammala shan magunguna na tsawon lokacin da aka kayyade a saboda rashin magungunan ko kuma tsadarsu, a yanzu an fara ganin kwayoyin cutar tarin fukar dake iya jurewa irin magungunan da ake amfani da su.

Majalisar Dinkin Duniya ta sanya kawar da Tarin Fuka nan da shekarar 2050 a zaman daya daga cikin gurorinta na Karni.

A wani rahoton dabam, Amurka ta fada jiya alhamis cewa ita ma ta kasa cimma gurinta na kawar da cutar tarin fuka kwata-kwata daga Amurka zuwa shekarar da ta shige ta 2010. Cibiyar Yaki da Cututtuka ta Amurka ta ce yawan masu fama da tarin fuka ya ragu da kashi 4 cikin 100 a shekarar da ta shige, amma har yanzu akwai mutane fiye da dubu 11 masu dauke da wannan cuta a nan Amurka a 2010, akasari a jihohin California, da Florida, da New York da kuma Texas.

XS
SM
MD
LG