Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akwai Bukatar Rage Illar Shan Barasa


Kantin barasa
Kantin barasa

Sabon rahoto na Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya yace barasa tana kashe mutane miliyan biyu da rabi kowace shekara a fadin duniya

Wani sabon rahoton da Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya ta kaddamar ya ce ana bukatar sabbin manufofi domin rage illar da shan barasa fiye da kima keyi ga lafiyar jama'a. Yin amfani da barasa fiye da kima tana kashe mutane miliyan biyu da rabi kowace shekara, da janyo rashin lafiya da rauni ga wasu da dama, yayin da ta ke kara shafar matasa da masu shanta a kasashe masu tasowa.

Ana fassara "yin amfani da barasa fiye da kima" a zaman shan barasa ta yadda har zata shafi lafiyar wanda ya sha.

Wannan rahoto da aka lakabawa suna "The Global Status Report on Alcohol and Health" ya nazarci shaidar da ake da ita ta shan barasa, da illolinta ga lafiya da zamantakewar jama'a da kuma yadda hukumomi ke takalar wannan batu a kasashe, da yankuna da kuma duniya baki daya.

An gano cewa kusan kashi 4 cikin 100 na masu mutuwa a duniya kowace shekara, barasa ce take zamowa sanadinsu.

Kasashe da dama ba su da shirye-shiryen hana mutane shan barasa fiye da kima. An kara yawan matakan dakile tallar barasa da kuma tuki cikin maye a fadin duniya, amma kuma babu wasu matakan zahiri na hana mutane shan barasar.

Nazarin bayanai daga shekarar 2001 zuwa 2005 ya nuna cewa yawan masu shan barasa bai karu ba a kasashen nahiyar Amurka, da Turai da Gabashin tekun bahar Rum da kuma yankin yammacin tekun Pacifc. Amma an ga karuwar yawan masu shan barasa sosai a nahiyar Afirka da yankin kudu maso gabashin Asiya a cikin wadannan shekarun biyar.

Amma kuma duk da cewa ana shan barasa a kowane lungu na duniya, a zahiri yawan mutanen da ba su shan ta sun fi masu sha yawa a duniya. Rahoton ya gano cewa a shekarar 2005, kusan rabin mazaje a fadin duniya ba su sha barasa ba, yayin da kashi 67 cikin 100 na mata ba su sha barasar ba.

Kasashen larabawa na Arewacin Afirka da kuma kasashen kudancin Asiya su ne suka fi gujewa shan barasa a duniya.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG