Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, ya ce kula da samari da 'yan mata masu shekara 10 zuwa 19 zai taimaka sosai wajen karya lagon talauci da rashin daidaito. Wannan yana kunshe cikin Rahoto Kan Matsayin Yara A Duniya na 2011 na asusun.
Irin kulawar da aka nuna sosai a cikin shekaru 20 da suka shige ta sa an cimma tazara sosai wajen kyautata rayuwar yara har zuwa shekaru 10. Raguwar kashi 33 cikin 100 na yara 'yan kasa da shekara 5 dake mutuwa da aka samu a duniya ta nuna cewa an ceto rayukan yara da dama. A fadin duniya, an gano cewa yawan yara mata dake zuwa makarantun firamare ya kamo na yara maza.
Amma a gefe guda, ba a cimma tazarar a zo a gani ba game da kyautata rayuwar matasa. Akwai matasa fiye da miliyan 70 wadanda ya kamata a ce yanzu su na makarantun sakandare, amma kuma ba su zuwa makaranta. Kuma har yanzu yara mata su na bayan yara maza wajen zuwa makarantun sakandare a fadin duniya. Idan ba ilmi, samari maza da mata ba zasu samu irin ilmi ko sana'ar da suke bukata domin fara rayuwa mai amfani ba.
Babban darektan asusun UNICEF, Anthony Lake, yace "muna bukatar kara mayar da hankali wajen kaiwa ga matasa, musamman mata, mu zuba jari a fagen ilmi, kiwon lafiya da wasu matakan na sanya hannun matasan a kokarin kyautata musu rayuwa."
Kashi 88 cikin 100 na samari 'yan shekaru 10 zuwa 19 su na zaune ne a kasashe masu tasowa. Da yawa daga cikinsu su na fuskantar kalubale sosai.
Anthony Lake yace, "miliyoyin samari da 'yan mata a fadin duniya su na jiran mu dauki matakai. Bai wa matasan abubuwan da suke bukata domin inganta rayuwarsu zai haifar da al'umma mai karfin tattalin arziki wadanda zasu iya bayar da cikakkiyar gudumawa ga rayuwar kasashe da al'ummarsu."