A ranar da ake bukin "Ranar Ruwa" a fadin duniya, Amurka da Bankin Duniya sun rattaba hannu a kan wata yarjejeniya da nufin tabbatar da kyawu da kuma tsaron ruwa a fadin duniya.
A jiya talata, sakatariyar harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton, da shugaban Bankin Duniya, Robert Zoellick, suka rattaba hannu kan wannan yarjejeniya a Washington, a wani bangare na Ranar Ruwa ta Duniya.
A wani gefen kuma, wata kungiyar rajin kare mata mai suna "WASH Advocacy Initiative" wadda ke da cibiya a birnin Washington, ta yi kira ga jami'an gwamnatin Amurka da kamfanoni tare da sassa masu zaman kansu, da su tsara manufofin da ake bukata domin kawo karshen matsalar karancin ruwa da tsabtar muhalli a fadin duniya.
Wannan matsalar, in ji kungiyar, tana yin mummunar illa ga lafiya, da ilmi, da tattalin arziki da kuma kuzarin dubban miliyoyin mata, manyansu da kananansu, a fadin duniya fiye da kowane jinsi na al'umma.
Gary White, shugaban kungiyar ta WASH Advocacy Intiative, kuma daya daga cikin wadanda suka kirkiro dandalin "water.Org" a kan Internet, yace wannan matsala ta ruwa da rashin tsabtar muhalli tana kashe mutane fiye da dukkan mutanen da ake kashewa da bindigogi a yake-yake.
A cikin kowane minti daya, yara uku su na mutuwa a sanadin wata cutar da ake samu daga ruwa, wadda kuma ana iya yin rigakafinta cikin sauki. Samar da ruwa mai kyau da tsabta, tare da tsabtace muhalli zasu iya kyautata rayuwar al'umma, kuma mata, manya da kanana, wadanda ke shafe awoyi a kullum wajen debo ruwa maras kyau daga kogi ko rijiya ko korama, zasu iya samun sukunin yin wasu abubuwan na inganta rayuwarsu.
Alal ga misali, a lokacin da aka ja famfo aka kuma gina wuraren ba-haya a wata makaranta a Najeriya, yawan yaran dake zuwa makarantar ya karu daga 320 zuwa 538.