Tawagar ta fito da rahoto mai dauke da shawarwari 30, a ciki akwai wasu muhimmai guda bakwai.
Na farkon shi ne, kungiyar ta EU wacce ta tura tawaga a zaben, ta yi kira ga hukumar zaben Najeriay da ta dauki kwararan matakai na inganta tsarin zabe da ma yadda za a rika tara sakamakon zaben.
A cewar tawagar, ya kamata a yi amfani da sababbin hanyoyin kimiya da fasaha wajen tattara sakamako, tun daga unguwanni zuwa gundumomi, saboda yin haka na iya ba da dama a amince da sakamakon ba tare da ta da jijiyar wuya ba.
Shugabar Tawagar Maria Arena ta ce, sun lura cewa akwai matsaloli na gudanarwa da ya shafi yadda al'umma suka fito wajen yin zaben, saboda haka suke ba da shawarar a kara yin kwaskwarima a daukacin harkar zaben har zuwa hukumar zaben, tare da sa ido a irin rawar da jami'an tsaro ke takawa a lokutan zabe.
Arena ta kara da cewa, a nasu nazarin, zaben na shekara 2019 na tattare da tashin hankali domin ita kanta hukumar zabe ta ba da rahoton kai hare-hare akan jami'anta da suka gudanar da zaben, musamman a Jihar Rivers da ke Kudu maso kudancin Kasar, wannan ya tsorata daukacin mutane har da jami'an da suka sa idanu.
Sannan shugabar tawagar ta ce a yi kokari a ba mata dama domin su taka rawa a fagen Siyasar Najeriya.
Maria ta ce, sun lura a zaben bana mata basu tsaya zabe sosai ba, inda ta yi kwatance da wasu kananan kasashe da ke makwabtaka da Najeriya, tana mai cewa sun ba wa mata dama da yawa, soboda haka suke samun ci gaba mai ma'ana.
Ta ce Najeriya ta jajirce ita ma, ta ba mata dama a dama da su.
Tawagar mai dauke da jami'ai 40 ta kewaye jihohin Najeriya 36 har da Birnin Tarrayya na Abuja, domin bin abubuwan da suka wakana a lokacin zaben kuma sune aka hada a rahoton.
Ga cikakken rahoton wakiliyar Muryar Amurka Medina Dauda.
Facebook Forum