Sanin babban kusancin dake tsakanin talakawa da masu wakilancin al’umma a majalisun dokoki, ya sa majalisar dinkin duniya da kungiyar hadin kan majlisun kasashen duniya UIP shirya wannan taro na hadin guiwa da majalisar dokokin jamhuriyar Nijar, domin samun hanyoyi da matakan cimma nasara kan matsalolin ta’addanci inji dan majalisar dokokin kungiyar CEDEAO, Boukary Sani Zilly.
samun hadin kan majalisun dokoki wajen daukar wasu mahimman matakai a kasashen dimokradiyya wani abu ne da ya zamar wa gwamnatoci tilas, saboda haka mataimakin shugaban majalisar dokokin Nijar, Iro Sani ke cewa, majalisu na da rawar takawa a yaki da ta’addanci.
Zurfafa bincike domin gano ainihin tushen makaman da ‘yan ta’adda ke amfani da su na daga cikin hanyoyin da ake ganin zasu taimaka a murkushe aiyukan ta’addancin da suka addabi jama’a.
Kasashen Algeria, Burkina Faso, Cameroun, Cote d’ivoire, Djibouti, Mali, Marocco, Nijar, Senegal da Chad ne, suka halartar wannan taron da za'a kammala gobe juma’a, yayinda Italia da kenya da Autriche ke wakiltar kwamitin tuntuba na kungiyar UIP a matsayin ‘yan kallo.
A saurari cikakken rahoton wakilin Muryar Amurka Souley Moumouni Barma.
Facebook Forum