Wakilin Majalisar Dinkin Duniya dake aiki a bangaren mata Peter Mancha yace sun lura cewa shigar da mata harkokin tattaunawa domin samun zaman lafiya zai yi kyakyawar tasiri.
Yace ba a Najeriya kadai ba a duk duniya idan ana son a samu cigaba a zaman lafiya dole ne a sa mata saboda a samu cigaba. Dalili ke nan da wani kudurin Majalisar Dinkin Duniya yace duk lokacin da ake son tattaunawa akan zaman lafiya dole ne a yi da mata. Mata nada baiwar kawo zaman lafiya fiye da maza.
Wasu dake hulda a tsakanin jama'a sun furta irin matsalolin da mata suka fada ciki. Florence Jambol shugabar matan Berom tace matsalolin da suke fuskanta suna da dama. Misali idan an kashe mazajensu samun abinci kan yi masu wuya. Mata kan samu damuwa idan an tadasu daga matsuguninsu ko wurin sana'o'insu. Wasu matan saboda tsananin azaba sukan taba karuwanci. Tana fata gwamnati zata taimaki mata da jari da kuma gina masu 'yan gidaje da zasu samu su tsuguna cikinsu.
Hajiya Yamuka Abubakar Abdullahi da ta wakilci Jama'atu Nasril Islam bangaren mata tace mata ne ke ciki su haihu a kuma kashe masu 'ya'yan. Mace ce zata yi aure a kashe mata miji. Idan wadannan abubuwa sun faru sai a barsu babu mai kula da dasu. Idan maza zasu tsaya su yi aiki tsakaninsu da Allah yakamata su goya ma mata baya a nemo mata dake fuskantar matsaloli domin a samu nasara.
Ga karin bayani