Domin ma’aikatar Man Fetur ta kasa na cewa tana da isasshen Mai da zai wadaci kasar na tsawon lokaci. To sai dai a zahiri mafi yawan gidajen Man za a iske babu Man Fetur, wasu kalilan din dake da shi za a iske dogayen layukan motoci, an kuma bar yan Bunburutu suna cin kasuwarsu babu babbaka.
Wakiliyar Muryar Amurka Mandina Dauda, ta zanta da wasu masu sayar da Man, inda suka shaida mata cewa suna sayar da lita 10 ta Mai a kan N1600 zuwa N1800, sun kuma ce wasu ne ke zuwa su saro sannan su sayar musu da shi.
Wannan hali da kasar ta tsinci kanta ciki shine yasa kungiyar kwadago ke cewa zatayi zanga zanga, kamar yadda kwamarad Nasiru Kabir, na kungiyar kwadagon ya bayyanawa Madina.
Karamin ministan Man Fetur Emmanuel Ibekachikwu, yayi yunkurin kawo karshen matsalar Man Fetur din inda ya kafa wani kwamiti na mutane 14 kuma tuni sun fara aiki.