Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yar majalisar wakilan Amurka ta jagoranci tunawa da 'yan matan Chibok


Federica Wilson 'yar majalisar wakilan Amurka da ta sanya jajayen kaya daga kanta har takalminta domin tunawa da 'yan matan Chibok
Federica Wilson 'yar majalisar wakilan Amurka da ta sanya jajayen kaya daga kanta har takalminta domin tunawa da 'yan matan Chibok

‘Yar majalisar wakilai Frederica Wilson ta jihar Florida tayi wata shigar da zaka iya hangenta daga nesa, cikin jajayen kaya daga ka har kafa, ta tsaya a gaban majalisar tarayya jiya domin tunawa da cika shekaru biyu da sace ‘yammatan sakandaren Chibok sama da dari biyu da kungiyar Boko haram tayi a kauyen Chibok dake arewacin Majeriya.

Willson tana jagorantar wani zaman mako-mako a majalisar tarayyar inda ake kira da a saki yammatan. ‘Yan majalisar da suka halarci gangamin suma sun sa jajayen sutura kamar yadda masu zanga zanga a Najeriya suka yi.

‘Yammatan na Chibok suna wakiltar daruruwan yammata da mata da kungiyar Boko Haram ta sace tana yiwa fyade, da kuma daruruwan maza da kananan yara maza da aka raunata ko kuma aka kashe inji Wilson jiya Alhamis. Sama da mutane miliyan biyu da dubu dari suka kauracewa matsugunansu sakamakon tashin hankalin da kungiyar ke yi.

Wilson tace, ta kai ziyara Najeriya ta kuma ji labarin irin ta’asar da kungiyar tayi daga bakin wadanda abin ya shafa, da suka hada da yiwa mutane yankan rago. Ita da sauran ‘yan majalisar tarayyar suna allah wadai da jin cewa, yanzu kungiyar tana amfani da kananan yara mata ‘yan shekaru takwas a matsayin ‘yan kunar bakin wake a hare haren ta’addanci da take kaiwa.

Shugabar marasa rinjaye a majalisa Nancy Pelosi ta marawa Wilson baya, tare da wadansu ‘yan majalisa da kuma yammatan Sakandaren Chibok da suka sami zuwa karatu a nan Amurka.

Dan jam’iyar Republiccan a majalisar wakilai Chris Smith ya bayyana karara cewa, majalisar zata yi magana da baki daya ba tare da banbancin siyasa ba wajen ci gaba da yayata wannan batu. Yace kungiyar Boko Haram tana yaki da yara mata da kuma mata, sau da dama kuma tana farautar kiristoci ne a harin sai dai yanzu galibin wadanda take kaiwa harin Musulmi ne.

‘Yar jam’iyar Democrat a majalisa Barbara Lee ta goyi bayan cewa, akuba da ake gasawa ‘yammatan a hannun ‘yan Boko Haram tamkar wani sabon babin bauta ne. Wadansu kwararru a fannin ta’addanci sun hakikanta cewa, yammatan Chibok din, da kuma wadansu yammatan Najeriya da kungiyar ke garkuwa da su, suna nan da rai, kuma kungiyar Boko Haram tana tsare su da nufin neman tayin musaya dasu.

Wani sabon faifan bidiyo da ya fita kwanan nan ya nuna wadansu yammata goma sha biyar da aka ce ‘yammatan Chibok ne sanye da bakeken hijabi.

‘Yar jam’iyar Democrat a majalisar wakilai Sheila Jackson Lee tana kira ga majalisa ta samar da kudi domin taimakawa dangin yammatan da ake garkuwa da su, ta kuma sha alwashin ci gaba da fafatukar ganin an sako su an kuma murkushe kungiyar Boko Haram.

XS
SM
MD
LG