A Najeriya ana ci gaba da samun mabambantan ra'ayoyi dangane da batun rufe makarantun da wasu gwamnatoci suka yi a cikin wannan wata na Ramadan.
Gwamnatin jihar Kebbi da ke arewacin Najeriya, daya daga cikin jihohin da suka rufe makarantu ta ce, yin haka ba zai sauya tsarin kalandar karatu na shekara ba a jihar.
A farko makon nan jaridu na cikin gida har ma da na wajen Najeriya suka ruwaito korafi a kan wasu gwamnatocin arewacin Najeriya a kan rufe makarantu a lokcin watan Ramadan, abin da wasu ke ganin bai dace ba musamman idan aka yi la'akkari da cewa an jima ana alakanta yankin arewa da koma baya a fannin ilimin boko.
Jihohin da aka ruwaito sun rufe makarantun su ne Katsina, Kebbi, Kano da Bauchi inda aka rufe makarantu tun daga matakin firaiamare har zuwa sakandare wasu ma har na gaba da sakandare.
Kungiyar mabiya addinin kirista ta Najeriya ita ce ta fara nuna damuwa a kan daukar wannan matakin, domin a ganinta ba a yi wa yaran arewa adalci ba idan aka hana su karatu na tsawon kwanakin da aka rufe makarantun kamar yadda Rev. Joseph Hayab, shugaban kungiyar mabiya addinin kirista reshen arewacin Najeriya da Abuja ya fada.
A nata bangaren gwamnatin jihar Kebbi, daya daga cikin wadanda suka dauki wannan mataki ta ce ta yi hakan ne bisa damar da dokar kasa ta bayar.
Dokta Halimatu Muhammad Bande kwamishinar ilimin bai daya da na sakandare a jihar ta Kebbi, ta ce gwamnan jihar Dokta Nasir Idris wanda Malami ne da ya san ciki da wajen aikin malanta shi ya bayar da damar a rufe makarantu bisa dalilin da yake ganin shi ne maslaha, da kuma damar da doka ta ba shi na yin haka.
Sai dai kwamishinar ta ce wannan rufe makarantu ko kadan ba zai sauya tsarin kalandar karatu nas shekara ba ga makarantun jihar.
Shi kuwa shugaban kungiyar CAN yankin Arewa yana mai ganin kamata ya yi a aje duk wani batun addini ko kabila a rungumi gaskiya.
Masana dokokin kasa irin Barista Alkali Sidi Bello na ganin sha'anin ilimi abu ne da gwamnonin jihohi ke da cikakkar dama ta doka akai.
Sai dai a cewar shi, ba wannan ne abin damuwa ba dangane da wannan batun.
Yayin da dalibai a wadannan jihohin arewa hudu ke ci gaba da hutu, takwarorinsu na sauran jihohin kasar na ci gaba da zuwa makaranta suna karatu, su kuwa 'yan Najeriya na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu a kan batun inda suke kallonsa ta fuskoki mabambanta.
Saurari cikakken rahoton Muhammad Nasir daga Sokoto:
Dandalin Mu Tattauna