Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Takaddama Tsakanin Israila da Falasdinawa ta Cigaba tare da Zubar da Jini


Sojojin Israila sun tsare wani bafalasdine da ya samu rauni
Sojojin Israila sun tsare wani bafalasdine da ya samu rauni

Fada tsakanin Israila da Falasdinawa na kara kamari tare da zubda jini

Jiya Lahadi ma bata canza zani ba saboda Israila da Falasdina sun cigaba da kaiwa juna hari tare da zubda jini.

Yanzu an shiga mako na biyu da suke ta kaiwa juna hari.Harin da Israila ta kai zirin Gaza wanda tamkar martani ne, saboda rokar da Faladinawa suka harba, ya kashe wata mace bafalasdiniya mai juna biyu da 'yarta . Wasu ma'aikatan jinya sun ce sun mutu ne yayinda ginin da suka fake ciki ya rushe a kansu ya kashesu tare da raunata wasu..

Wani balarabe dan Israila ya afkawa mutane hudu da motarsa kafin ya diro ya kama sukar mutanen da wuka. Lamarin ya faru ne a arewacin kasar. Haka kuma wata bafalasdinya ta samu mugun rauni yayinda tukunyar gas ta fashe ta kuma tarwatsa motarta a wani wurin da jami'an tsaro ke duba ababen hawa a yankin West Bank inda yahudawa 'yan kama wuri zauna suke.

Firayim Ministan Israila Benjamin Netanyahu ya sha alwashin dakile abun da ya kira ta'adanci kodayake ya ki ya saurari yahudawa masu ra'ayin rikau dake kiransa ya dauki tsauraran matakai. Yana gudun kada ya rasa goyon bayan kasashen yammacin turai idan yayi hakan.

TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG