Firayim Ministan Israila ya sha alwashin daukan tsauraran matakai akan Falasdinawa saboda harin da suke kai wa Yahudawa.
Jiya Alhamis Firayim Ministan ya yi wani taro da 'yan jarida da jami'an tsaron kasar bayan da wasu Falasdinawa suka soki akalla Yahudawa biyar da wuka.
Firayim Minista Netanyahu ya shaidawa 'yan jarida cewa Hamas da hukumar Falasdinawa da wata kungiyar Musulmi suke harzuka rikicin. Wadannan ukun su ne suke rura wutar rikici a yankin.
A wani bangaren kuma Yahudawa masu ra'ayin rikau sun bukaci Firayim Ministan ya dauki tsauraran matakai akan Falasdinawan tare da gina karin gidajen ma 'yan share wuri zauna a gabar yammacin kogin Jordan.
Kamar yadda ya sha alwashi Benjamin Netanyahu ya bayyana tsauraran matakan da zai dauka ciki har da harramtawa maza daga 'yan shekaru 20 zuwa 50 kai ziyara Mallacin Al-Aqsa.
Netanyahu bai tsaya nan ba. Zai haramtawa manyan shugabannin Israila da Larabawa 'yan siyasa kai ziyara Masalacin.
Shugaba Abbas ma ya goyi bayan turjewar Falasdinawan amma cikin lumana.