Firayim Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, yace hukumomi sun sakarwa jami'an tsaron kasar mara yayinda suke tunkarar karuwar tashe tashen hankula daga Falasdinawa.
"Mun kyale jami'an tsaro su dauki matakai masu tsanani kan wadanda suke jifa da duwatsu da kuma kwalaben da aka durawa man fetur ko wani abu sannan aka cunna masu wuta", inji Netanyahu, jim kadan kamin a fara taron majalisar ministocin kasar kan batun tsaro a jiya Litinin.
Dama tuni ya ce za'a hanzarta rusa gidajen 'yan ta'adda, sannan za'a daure wadanda ake zargi da ta'addanci ba tareda an gurfanar da su ba tukun.
Ahalinda ake ciki kuma, shugaban yankin Falasdinu Mahmoud Abbas ya gana da shugabannin tsaro na yankin a jiya Litinin,, yana mai kira garesu cewa su dakile karuwar tarzoma, kuma kada su kyale takalar da gwamnatin Isra'ila take yi ta shafi ayyukansu.
A lamari na baya bayan nan a jiya Litinin, dakarun Isra'ila sun harbe suka kashe matasan Falasdinawa biyu wadand suke harbi da duwatsu a yammacin kogin Jordan. Hakan nan jami'an tsaron na bani-Yahudun suka kama Falasdinawa biyar, dangane da harbe yahudawa biyu, wani mutum da matarsa.
Rikici tsakanin Isra'ila da Falasdinawa yayi tsanani cikin makon da ya gabata, musamman kan masallacin al-Aqsa, wanda Yahudawa suke kira Temple Mount.