Tsohon alkali kuma mataimakin magatakardar babban kotun jihar Adamawa Barr. Husseini Duraki Kazir ya ce kamata ya yi idan lauya ko dansanda ya nemi a dage sauraron shara'a sau uku alkali ya kori karar bisa hujjar rashin kwakkwarar shaidu kuma ya sallami wanda ake tuhuma har sai lokacin da suka kammala tattara shaidu.
Limamin darikar Katolika Bishop Stephen Dami Mamza shugaban daya daga cikin kungiyoyi jinkai wa firsinoni ya nuna takaicinsa kan yadda fannin shara'a ke fifita masu hannu da shuni. yayin da lauya mai zaman kansa Barrister Sunday Wagira ke kallon lamarin daga kowane bangare ya jajirce wajen sauke hakkin da kundi tsarin shara'a ya ba shi.
Da yake kare jamiansa daga zargin yiwa shara'a karar tsaye. jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yansanda ta jihar Adamawa DSP Othman Abubakar gani yake kamata ya yi a fadada gidajen yari saboda karuwar masu aikat laifuffuka.
Ga rahoton Sanusi Adamu da karin bayani.