Wata sanarwar da gwamnatin kasar ta bayar yau, tace,duk da haka sojojin kasar zasu ci gaba da fafatawa da take yi da kungiyoyin ISI da al-Qaida, da wadanda suke alaka da su.
Shirin tsagaita wutar da Amurka da Rasha suka gabatar bai shafi wadanndan kungiyoyin ta'addan ba,kuma duk wata kungiya an bata wa'adi zuwa jumma'a ta bayyana matsayarta kan yarjejeniyar. Babbar gamayyar kungiyoyin 'yan hamayya jiya litinin ta bayyana cewa ta amince da shirin tsagaita wuta, muddin dai an amince da bukatar da ta gabatar na janye dukkan kawanya, da kyale jigilar kayan ayyukan ceto d a agaji, da kuma kawo karshen jefa bama-bamai kan farar hula.
A cikin wata sanarwa ta hadin guiwa da da suka fitar a jiya Litinin, Amurka da rasha sun ce karkashin shirin tsagaiata wutan,sassa d a suke gaba da juna zasu takaiata amfani da karfi ne kawai wajen kare kansu idan aka kai musu hari. Haka nan duka sassan zasu amince ba zasu hana kungiyoyin da suke aikin jinkai da agaji walwala ba zuwa sassan aka yiwa kawanya.