A wata sanarwa da ya fitar, Ministan harkokin wajen kasar Rasha, ya ce wadannan hare-hare da kungiyar IS ta dauki alhakin kaiwa, na bukatar kasashen wajen su maida martani
Wasu hare-hare da aka kai a birnin Damascus a jiya Lahadi sun halaka akalla mutane 83, yayin da wani harin bam na daban ya kashe mutane 59 a Homs.
Yanzu haka Rashan da Amurka, na kokarin su rarrashi bangarorin da ke takaddama a kasar ta Syria, da su amince da wani sabon shirin tsagaita wuta.
Sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry a jiya Lahadi, ya ce an cimma wata matsaya ta wucin gadi da kasar Rasha wacce za ta fara aiki nan da wasu ‘yan kwanaki
Kerry ya gana ne da twakaran aikinsa Sergie Lavrov ta wayar talho, inda ya ce bangarorin biyu sun amince da tsarin tsagaita wutar, ba tare da sun bayyana yadda za a tafiyar da shirin ba.