Ana sa ran kayayyakin za su isa Madaya, wani gari da ke kusa da iyakar Lebanon da kuma Fuaa da Kafraya da ke Lardin Idlib a kusa da iyakar Turkiyya.
Wannan kai doki da ake shirin yi, na samun hadin gwiwar kungiyar ba da agajin gaggawa ta Red Cross da reshen ta na Syria da kuma Majalisar Dinkin Duniya, bayan da hukumomin Syrian suka amince a bar kayayyakin su wuce.
Rahotanni sun ce fararen hula a wadannan yankuna, sun shiga halin kakani-kayi, yayin da fadan da ake yi da ‘yan tawaye da dakarun shugaba Bashar Al Assada ya shiga kusan shekara ta biyar.
Baya ga haka, akwai sauran bangarorin da ke cikin wannan fada wadanda suke adawa da gwamnatin ta Syria.
‘Yan tawayen Syria dai suke rike da garin na Madaya, lamarin da ya sa dakarun kasar suka datse hanyar kaiwa ga garin, wanda ke dauke da mutanme dubu 42.