Kungiyar da take rajin kare hakkin Bil'adama a Syria mai cibiya a Ingila, tace mata da yara suna cikin wadanda hare haren suka rutsa da su, a farmakin da dakarun gwamnatin suka kai jiya Alhamis, kan kauyen da ake kira Hammouriyeh.
Wasu da dama kuma sun jikkata.
Ahalinda ake ciki kuma,ministan harkokin wajen kasar Walid Muallem, yace a shirye kasarsa take ta shiga taron sulhu kan rikicin kasar da za'a yi a Geneva, "ba tareda shishigin kasashen waje ba,"mako daya bayan da kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da wani shirin sulhu da kasa da kasa ke goyon baya, da zummar kawo karshen yakin basasar da kasar take fuskanta.
Ministan ya bayyana haka ne yayinda yake magana jiya Alhamis a Beijing, inda ya gana da tawakaran aikinsa na China Wang Yi. Muallim yace, tawagar gwamnati zata shirya da zarar ta sami jerin sunayen mutanen da zasu wakilci 'yan tawayen.