Tashar wacce take koikoyon takwarorinta a Iraqi d a Syria, tana aiki akalla sa'a daya a wuni, inda yake jawo hankalin matsa wanda suke fama da kuncin rashin aikin yi, wanda ya kai kashi 24 cikin dari.
Rashin aikin yin, ya fi tsanani tsakanin matasan, wadanda ISIS take auna farfagandar akansu.
Ahalin yanzu, tashoshin da rediyon na ISIS yake yada farfagandarsu, anji yana yada take 'yancin kasar da wasu kade kaden gargajiya.
Kakakin gwamnan Nagarhar, ya gayawa Muryar Amurka cewa, hukumomin yankin sun sami nasarar tsaida aikace aikacen rediyon. Yanzu suna kokarin gano inda rediyon yake.
Amma wasu jami'ai a karamar hukumar suka ce, sai tayu wasu dakarun kasashen ketare ne suka taimkawa hukunomin yankin su rufe gidan rediyon.