Usman Alkali Baba wanda ya ce zai jagoranci rundunar 'yan sanda mafi girma a Afirka a daidai lokacin da Najeriya ke cikin halin tsaka mai wuya duba da irin tabarbarewar tsaro da ke akwai a kasa.
Ya ce kama daga aika aikar yan ta'adda, yan bindiga dadi, masu garkuwa da mutane don neman kudin fansa ya zuwa masu rajin ballewa daga Najeriya da ma sauran manyan miyagun tsararrun laifuka na nuna cewa akwai aiki ja a gabansa.
Amma ya ce da irin zakakuran jami'ai da ake da su a rundunar to za a iya shawo kan matsalolin.
Karin bayani akan: Usman Alkali Baba, DIG, Mohammed Abubakar Adamu, yan bindiga, Afirka, Nigeria, da Najeriya.
Yayin da sabon sufeton ya fara aiki gadan-gadan, tuni lauyan nan dan gwagwarmaya Barrister Maxwell Okpara ya shirya tsaf don garzayawa kotu don kalubalantar nadin da aka yi wa Usman Alkali Baba.
A cewarsa, nadin ya sabawa sashe na 7 na dokar aikin 'yan sanda ta shekara ta 2020.
Barrister Okpara dai shi ne wanda ya kai gwamnatin tarayya kara inda yake kalubalantar karin wa'adin wata uku da aka yi wa tsohon sufeta janar na 'yan sanda M.A. Adamu, shari'ar da za a yanke hukunci mako mai zuwa.
Saurare cikakken rahoton Hassan Maina Kaina a sauti: