Sojojin Najeriya sun dauki kwanaki suna ta kai farmaki ga sansanonin tsagerun Niger Delta, dake jihohin Lagos da Ogun, farmakin mai taken “operation a watse” mayakan sama sunyi ta sakar boma bomai a yankin Arepo dake jihar Ogun, dake zama tungar tsagerun da ma wasu sassan da suke a jihar Lagos.
Haka kuma sojojin ruwan Najeriya na tunkarar tsagerun ta cikin ruwa yayin da dakaru suka zagaye yankunan. Daraktan yada labarai na hedkwatar sojojin Najeriya, Birgediya Janal Rabe Abubakar, yace barin wuta da sojojin ke yi a jihohin biyu zai ci gaba.
Yan bindigar Niger Delta na kukan cewa yankunansu na fama da koma baya duk kuwa da dinbin kudin da gwamnatocin jihohin yankin ke karba da ga gwamnatin tarayya, a baya dai ministan wasanni da matasa Barister Solomon Dalung, ya ziyarci wannna yanki har ya fadawa wakilin Muryar Amurka Hassan Maina Kaina, cewa tabbas siyasar yankin ba ta da dadin ji domin babu wasu kayayyakin more rayuwa da al’ummar yankin zasu mora.
Saurari rahotan Hassan Maina Kaina.