Hukumomi sun tabbatar da mutuwar mutane 18, wanda 11 daga cikin su sojoji ne, bayan wata arangama tsakanin sojojin da mutanen Kopa ranar Alhamis din da ta gabata.
A wani taron manema labarai a yammacin ranar Lahadi, kwamandan runduna ta ‘daya da ke Kaduna, Manjo Janal Adeniyi Oyebade, yace cikin sojin 11 da suka rasa ransu har da ma wani Hafsa mai mukamin matemakin Laftanal, haka kuma akwai soja ‘daya da bindigogi biyar sunyi batan dabo a lokacin tashin hankalin.
Kawo yanzu dai sojojin sunce suna rike da mutane 50 da ake zarginsu da hannu a wannan mummunan kisa, sojojin dai sunce sunje ‘kauye Kopa ne domin binciko wasu mukamai da suka sami labarunsu kamar yadda babban daraktan tsaro na ofishin gwamnan jihar Neja, Kanal MK Mai Kundi Mai Ritaya, ya shaidawa Wakilin Muryar Amurka.
Mai Kundi, yace an samu wasu bayanan sirri dake cewa akwai makamai a Kauyen, kuma sojojin sun sami tarin makamai lokacin da suka isa kauyen, an dai ta fama da matsalar fashi da makami a hanyar kauyen.
Har yanzu dai ba a sami cikakken rahotan kwamitin da gwamnatin jihar Neja ta kafa domin binciken wannan al’amari.
Saurari cikakken rahotan Mustapha Nasiru Batsari.