Uwargidan shugaban Najerya Hajiya Aisha Buhari tace gwamnatin magidanta zai kawo karshen "almubazzaranci," da dukiyar al'uma a kasar.
Hajiya Aisha wacce ta zanta da shirin talabijin na MA da ake kira Africa 54 jiya jumma'a, lokacind a ta ziyarci Muriyar Amurka, tace nan bada jumawa ba, gwamnati zata samu kudade domin magance wasu muhimman bukatun al'uma, da zarar an kawarda cin hanci da rashawa wanda ya yiwa kasar katutu.
Haka nan Hajiya Aisha tayi magana kan ilmi daya daga cikin ayyuka data sa a gaba a matsayarta ta uwargidan shugaban kasa. Tace cikin shirye shirye data himmatu akansu harda yunkurin ganin an ciyarda yara abinci lokacinda suke makaranta, domin a karfafa musu guiwa.
Tace yanzu yara sun shiga makaranta "wadanda ada suke kan tituna suna gararamba da safe har maraice suna neman abunda zasu ci."
Hakan nan tace ta himmatu kan yaki da jahilci, wadda tace zai iya magance musabbabin fitintinu da irinsu Boko Haram da sauransu.