Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Wanke Manjo Hamza al-Mustapha


Manjo Hamza al-Mustapha a shekarar 2000
Manjo Hamza al-Mustapha a shekarar 2000

Babbar kotu a Lagos, ta ce ba a gabatar da wata kwakkwarar shaidar da zata nuna cewa manjo al-Mustapha da wadanda ake tuhuma sun kulla kashe Alex Ibru ba

Babbar kotu a Lagos, cibiyar kasuwanci ta Najeriya, ta wanke ta kuma sallami Manjo Hamza al-Mustapha daga tuhumar da aka yi masa ta neman kashe mawallafin jaridar Guardian, Alex Ibru.

Kotun da ta zauna dazu a birnin na Lagos, ta ce babu wata kwakkwarar shaidar da aka gabatar dake nuna cewa shi manjo al-Mustapha, tsohon babban jami'in tsaro na marigayi shugaba Sani Abacha, da sauran wadanda ake tuhuma sun hada baki domin su kashe Mr. Ibru.

Kotun ta ce shaidu guda 9 da masu gabatar da kararraki suka kawo gaban kotu, sun bayar da shaidar da ta rika sabawa da juna kan wannan lamarin, kuma akwai shaidar cewa su wadanda ake tuhumar an yi ta musguna musu har sai da suka furta aikata wasu abubuwan da ba su aikata a zahiri ba.

Sai dai kuma, har yanzu Manjo Hamza al-Mustapha yana fuskantar wata shari'ar ta kashe Kudirat Abiola da ake tuhumar cewa yana da hannu ciki.

XS
SM
MD
LG