Rundunar 'yan sandan Najeriya ta kori wasu 'yan sanda biyu, sannan ta rage mukamin na ukunsu, a bayan da aka gano cewar da hannunsu dumu-dumu a cikin abin fallasar nan na sace wata budurwa tare da yi mata fyade a cikin Kano.
A lokacin da yake tabbatar da hakan ga wakilin sashen Hausa na Muryar Amurka a Kano, kakakin rundunar 'yan sandan, ASP Magaji Musa Majiya, yace rundunar ta gudanar da bincike, ta kuma gano cewa PC Yusif Ibrahim Yusif da PC Salisu Mamuda su ne ummul haba'isin sace wannan yarinya da kulle ta na tsawon kwanaki 28, yayin da suka yi ta yi mata fyade. Yace an kore su daga aikin dan sanda.
Shi kuma dan sanda na uku, Sufeto Dantalle Mohammed, an rage masa mukami daga sufeto ya koma Saje, saboda an gano cewa ya na da labarin abinda ya faru, amma bai hana abkuwar hakan ba, kuma bai kai rahoton hakan ba.
kakakin 'yan sandan yace a bayan korar wadannan 'yan sanda biyu da aka yi, an mika takardarsu zuwa ofishin mai gabatar da kararraki na jiha domin a gurfanar da su gaban kotu.
A saurari hirar wakilinmu Mohammed Salisu Rabi'u da kakakin 'yan sanda ASP Magaji Musa Majiya, kan wannan lamarin.