Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Faransa Sun Kwace Filin Jirgin Saman Abidjan


Sojoji masu goyon bayan Alassane Ouattara a tsaye kusa da wani mutumin da ya ji rauni a Abidjan, asabar 2 Afrilu, 2011.
Sojoji masu goyon bayan Alassane Ouattara a tsaye kusa da wani mutumin da ya ji rauni a Abidjan, asabar 2 Afrilu, 2011.

An ce sojoji masu goyon bayan Ouattara daga sassan kasar su na taruwa a bayangarin Abidjan domin kaddamar da farmaki mai gaba-daya na kawar da Laurent Gbagbo daga kan kujerar mulki

Sojojin faransa sun karbe babban filin jirgin saman Abidjan a yayin da mayakan mutane biyu dake ikirarin shugabancin kasar Ivory Coast suke ci gaba da bai wa hammata iska domin kwace cibiyar kasuwancin ta kasar.

Sojojin na Faransa su na amfani da filin jirgin saman domin kwashe 'yan kasashen waje dake gudu daga Ivory Coast, tare da kawo karin sojoji 300 domin karfafa rundunar kiyaye zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya.

Sojoji masu yin biyayya ga mutumin da kasashen duniya suka ce shi ne shugaban Ivory Coast na halal, Alassane Ouattara, sun kwace akasarin yankunan kasar a cikin mako gudan da ya shige, kuma a yanzu an ga alamun su na shirye-shiryen kai farmaki na karshe domin kawar da shugaba Laurent Gbagbo daga cikin fadar shugaban kasa dake Abidjan.

An ayyana Mr. Ouattara a zaman wanda ya lashe zaben shugaban kasa na watan Nuwamba, amma Mr. gbagbo ya ki yarda ya sauka daga kan kujerar shugabancin.

Sojoji masu yin biyayya ga Ouattara sun isa bayangarin Abidjan daga arewacinta, kuma su na shirye-shiryen kaddamar da farmaki.

Wasu sojojin da a can baya suke yin biyayya ga Mr. Gbagbo sun ajiye makamai suka mika kawunansu ga Majalisar Dinkin Duniya, an kuma bayar da rahoton cewa wasunsu sun tsallaka iyaka suka shiga kasar Ghana.

Kasashen duniya sun yi kira ga dukkan bangarorin da su guji kai hare-hare a kan fararen hula.

XS
SM
MD
LG