Ana ci gaba da kazamin fada a Abidjan babban birnin kasar Ivory Coast yayinda ake ci gaba da yakin kwace iko kofar fadar shugaban kasa da kuma garin shugaba mai ci yanzu Laurent Gbagbo. Mazauna birnin sun boye a gidajensu ranar jumma’a yayinda mayakan mutumin da kasashen duniya suka ce shine ya lashe zaben shugaban kasa, Alassane Quattara suke musayar wuta da dakarun dake goyon bayan Mr. Gbagbo. An kuma gwabza fada a bayan shelkwatar tashar talabijin ta kasar abinda ya sa aka katse watsa shirye shiryen talabijin ranar Alhamis amma aka ci gaba da yayata hoton bidiyon goyon bayan Mr. Gbagbo jiya jumma’a da yamma. Babu tabbacin ko Mr. Gbagbo yana fadar shugaban kasa ko kuma wani wuri dabam. Wani mai ba gwamnatin shawara dake da zama a birnin Paris, Alain Toussaint ya bayyana jiya jumma’a cewa, Mr. Gbagbo bashi da niyar mika mulki. Kakakin cibiyar Majalisar Dinkin Duniya a Ivory Coast ya shaidawa Muryar Amurka cewa, cibiyar ta yiwa Mr. Gbagbo tayin fitar da shi daga kasar domin kawo karshen rudamin. An sanar da Mr. Quattara a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar a cikin watan Nuwamba, amma Mr. Gbagbo ya ki sauka daga karagar mulki ya ci gaba da rike iko da taimakon sojoji. Sai dai mayakan dake goyon bayan Mr. Quattara basu fuskanci wata tankiyar kirki daga dakarun Mr. Gbagbo ba lokacinda suka kai sumame Abijdan ranar alhamis, bayan gumurzun da suka yi a fadin kasa suka rika kwace birane. Ranar jumma’a, cibiyar agaji ta Red Cross tace a kalla mutane 800 aka kashe a fadan na ranar alhamis a wani gari dake yammacin Ivory Coast. Babu tabbacin wanda ke da alhakin kisan.
Fada ya kazance a kofar fadar shugaban kasar Ivory Coast yayinda ake kokarin kwace iko.