Ma’aikatar harkokin wajen Faransa ta bada sanarwar cewa tana kokarin tattara dukkan ‘yan Faransa mazauna kasar Ivory Coast da niyyar kawshesu zuwa gida. Yanzu ana tattarasu ne a cibiyoyi uku dake hannun kulawar sojin Faransa a birnin Abidja. Wadannan cibiyoyin kuwa sun hada harda barikin sojin faransa dake tashar jiragen ruwa ta Bouet, da kuma Otel din Wafou dake yankin kudanci da kuma ofishin jakadancin Faransa dake Arewa. Akwai ‘yan Faransa mazauna birnin Abidja sama da dubu goma sha biyu an kumaji Ministan tsaron Faransa Gerard Longuet na cewa jami’an Faransa na kokarin shirya kwashe Faransawan kusan a lokaci guda domin maidasu gida, amma har yanzu dai Gwamnatin faransa ta tsaida wata shawarar yin hakan ba tukuna.
A ran lahadin da ta gabata ce dakarun Faransa suka kwace Filin Jirgin Saman Abidjan, a dai dai lokacin da bangarori biyun da ba su ga-maciji-da-juna ke ta gwabzawa don neman mallake babban birnin kasuwancin kasar.
Sojojin Faransa na amfani da filin jirgin saman don kwasar ‘yan kasashen waje masu tserewa daga Ivory Coast, da kuma shigowa da karin sojojin kasashen waje su wajen 300 don tallafawa sojojin kiyaye zaman lafiyar Majalisar Dinkin Duniya.
Dakarun da ke biyayya ga wanda kasa da kasa ke goyon baya a matsayin shugaban kasa Alassane Ouattara sun kwace akasarin kasar tun daga makon da ya gabata, kuma a yanzu suna yunkuri na karshe domin fatattakar bijirarren shugaba Laurent Gbagbo daga Fadar Shugaban kasa da ke Abidjan. An bayyana Mr Ouattara a matsayin wanda ya sami nasara a zaben watan Nuwamba, to amman Mr. Gbagbo ya ki mika ragamar iko.
Kasashen duniya dai na kiraye-kiraye ga bangarorin biyu da cewa kar su kai hari kan fararen hula.