Mazauna Abidjan, birni mafi girma a kasar Ivory Coast sun ce kazamin fada ya barke a kusa da fadar shugaban kasar, yayin da mayaka masu yin adawa da shugaba Laurent Gbagbo dake kan kujerar mulki suka kutsa cikin birnin.
'Yan tawaye masu goyon bayan mutumin da kasashen duniya suka yi na'am da shi a matsayin shugaban Ivory Coast na halal, Alassane Ouattara, su na kuma gwabza kazamin fada a kusa da hedkwatar tashar telebijin ta kasar. Kamfanin dillancin labaran Reuters yace ba a iya kama tashar telebijin din yanzu haka.
A cikin wannan makon, sojoji masu yin biyayya ga Ouattara sun ratsa fadin kasar, suka kwace birane da garuruwa masu yawa, kuma a yawancin lokuta ba tare da fuskantar adawa ko fada daga sojojin Gbagbo ba.
Tun da fari alhamisa, sojojin kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya sun kwace filin jirgin saman Abidjan, yayin da Faransa ta ce sojojinta su na yin sintiri a wasu sassan birnin Abidjan, inda aka fara balle kantuna da gidaje ana kwasar ganima.
Afirka ta Kudu kuma, ta ce babban hafsan sojojin Mr. Gbagbo da matarsa da 'ya'yansa, sun nemi mafaka a gidan jakadan Afirka ta Kudu dake Abidjan alhamis din nan.
Amurka da Majalisar Dinkin Duniya da Faransa, wadda ta yi ma Ivory Coast mulkin mallaka, da kuma jami'an gwamnatin Mr. Ouattara duk sun yi kira ga Mr. Gbagbo da ya sauka.
Mr. Gbagbo ya kekasa kasa ya ki jin kiraye-kirayen cewa ya sauka daga kan mulki tun lokacin da aka ayyana cewar Alassane Ouattara shi ne ya lashe zaben shugaban kasa na watan Nuwamba.
Alhamis, gwamnatin Mr. Ouattara ta bayar da sanarwa cewa ta kafa dokar hana yawon dare a Abidjan, ta kuma bayar da umurnin rufe dukkan iyakokin kasar.
Jami'an gwamnatin Mr. Ouattara dai sun yi hasashen cewa nan da 'yan sa'o'i kadan zasu iya kawar da Mr. Gbagbo daga kan karagar mulki.