Sojojin Amurka sun janye daga sansanninsu mafi girma a Siriya Jiya Lahadi, yayin da Sakataren Harkokin Tsaron Amurka, Mark Esper, ke cewa duk sojojin Amurka da ke janyewa daga Siriya za a tura su ne zuwa yammacin Iraqi don su ci gaba da kai hare hare akan ‘yan ta’addan IS.
Esper ya ce sojojin Amurka sama da 700 za a tura su zuwa Iraqi, kuma ba za su dawo “gida” ba kamar yadda Shugaban Amurka, Donald Trump ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa za su yi.
Esper bai kau da yiwuwar Amurka ta rika ketarowa daga Iraki ta na kai samame kan 'yan ta'adda a Siriya ba. To amma ya ce za a dau lokaci kafin a tsara yin hakan kuma tsarin zai hada da tattaunawa da kawayen Amurka na NATO cikin kwanaki masu zuwa. Sannan ya ce idan sojojin Amurka suka koma Siriya za su samu kariya daga jiragen saman Amurka.
Facebook Forum