Mayakan Siriya da ke samun goyon bayan Turkiyya sun fafata da mayakan da Kurdawa ke jagoranta a sassa da dama na arewa maso gabashin Siriya a jiya Asabar, inda wasun su su ka yi ta ketara iyaka daga kasar Turkiyya su na kai hare-hare kan wasu kyauyuka a Siriya, a cewar wata majiya da ke sa ido kan wannan yakin.
Bangarorin biyu na zargin juna da takalo fadan, wanda ke barazana ga yarjajjeniyar da Amurka ta taimaka aka cimma.
Kwanaki wajen biyu kenan da cimma yarjajjeniyar kwance damara ta tsawon kwanaki biyar, amma bangarorin biyu sun cigaba da musayar wuta a sassan muhimmin garin nan na Ras al-Ain da ke daura da kan iyaka. Babu wata alamar janyewar sojojin da Turkiyya ke jagoranta daga wuraren da su ka ja daga a gefen kan iyakar Siriya da Turkiyya, kamar yadda yarjajjeniyar da aka cimma tsakanin Amurka da Turkiyya ta tanada.
Ma’aikatar Tsaron Turkiyya ta ce ta na mutunta yarjajjeniyar matuka, kuma da ita da Amurka su na tuntubar juna akai-akai saboda tabbatar da dorewar kwanciyar hankali. Ma’aikatar Tsaron ta Turkiyya ta zargi mayakan da Kurdawa ke jagoranta da kaddamar da hare hare har sau 14 cikin sa’o’i 36 da su ka gabata, akasari a cikin birin Ras al-Ain, wanda ya zama turmin tsakar gida sha lugude ga bangarorin da ke gwabzawa.
To amma, su kuma Kurdawan, kira su ka yi ga Mataimakin Shugaban Amurka Mike Pence da ya tabbatar ana aiwatar da yarjajjeniyar, su na masu cewa Turkiyya ta kasa mutunta tanajin yarjajjeniyar, kuma ta cigaba da barin wuta kan birnin na Ras al-Ain.
Facebook Forum