A wata sanarwa da mai ba shugaban shawara akan harkokin yada labarai Femi Adesina ya fitar, ya bayyana cewa babu yadda za’a yi Shugaba Buhari da ya kasance uba ga ‘yan Najeriya wanda kuma ‘ya’yansa ke cikin rukunnin matasa, ya fito ya yanke hukuncin rashin tabbacin kwarin akan jimillan matasan kasar. Wannan kawai maganganun ‘yan ‘siyasar ganganci’ ne masu son siyasantar da komai.
Jiya ne dai a yayin taron kasashe rainon Ingila, Shugaba Buhari ya bayyana cewa, “akasarin matasan Najeriya zaune suke suna jiran a yi mu su komai na ababen more rayuwa don suna ganin kasar na da arzikin mai.”
Wadannan kalamai sun haddasa cece-kuce a cikin kasar inda har wasu ke tir da furucin na Buhari, don a ganinsu bai kamata ayi wadannan kalaman a idon duniya ba.
Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar shima ya fito yana sukar kalaman da cewa, “Ba zan taba kiran matasan Najeriya a matsayin cima zaune ba. Saboda ina da masaniya, kuma ina da dubban matasan da ke aiki a karkashina a fadin Najeriya, wadanda suka zama kaso bayar daga cikin dari na nasarar da muke samu.”
Shi kuma tsohon mataimakin shugaban babban bankin Najeriya, Kingsley Moghalu wanda ya bayyana niyyarsa ta tsayawa takarar shugabancin Najeriya cewa yayi, “Mu daina tambayar matasanmu dalilin da yasa kafafuwansu suka yi budu-budu da kura, alhali ba mu basu takalman rufesu ba”.
Alkalumma na nuni da cewa, Najeriya na daga cikin jerin kasashen da mutanenta ke cikin kangin talauci da kimanin kashi 70 cikin 100, wanda mutane na rayuwa ne ka a kasa da darajar dalar Amurka daya a rana bisa alkalumman Majalisar dinkin duniya.
Cibiyar kididdiga ta Najeriya ta bayyana cewa rashin aiki a kasar ya tashi daga kashi 14.2 cikin 100 zuwa kashi 18.8 cikin dari a shekarar 2017. Matasa da dama na kammala karatun gaba da sakandare amma babu aikin yi, to wannan laifin wanene?
Masana sun bayyana cewa ana samun sabani ne kan bukatar tattalin arziki da abubuwan da ake koyarwa a jami’u, ta yadda matasa ke fitowa ba su da kwarewar ayyukan da ke kasa suna jiransu.
Wani mai sharhi akan al’amuran yau da kullum, Aminu Gamawa cewa yayi,
Facebook Forum