Alhaji Dayyabu Salisu Sa’adu shugaban reshen jihar Kano na kungiyar masu cinikayyar kayan tufafin blouse, ya ce daga garin Onitsha zuwa Kano akwai wurare takwas da ‘yan kwastam ke tsayawa.
A kowane wuri cikin takwas din suna biyan N5,000 akan kowace mota, kuma akalla motocin 'yan kasuwa sama da 15 suke bin hanyar zuwa Kano a cewar 'yan kasuwan.
Ya kara da cewa hanyar Legas ta fi muni inda kwastam ke da wurare 14 kuma kowanensu sai sun biya sama N9,000 kan kowacCe motar kaya.
Sa'adu ya kara da cewa baya ga ’yan kasuwar Kano, Jami’an na Kwastam na karbar na goro a hannun takwarorinsu ‘yan kasuwa na jihohin Niger da Kaduna da Pilato da Katsina da sauran su.
A martanin da hukumar ta kwastam ta mayar, Mr. Joseph Attah, Kakakin hukumar kwastam mai shalkwata a birnin tarayya Abuja ya ce za su hukumta duk wani jami’insu da aka samu yana irin wannan dabi'ar.
Ya ce za su gudanar da bincike cikin sirri su tabbatar da lamarin domin su dauki matakan da suka dace.
Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari da karin bayani
Facebook Forum