Kungiyar ta zargi ‘yan sanda da hana kai abinci ga wadanda aka tsare a ofishin jami’ai masu yaki da ‘yan fashi da ake kira SAS su 150, wadanda suka ce sai bayan da aka matsa lamba aka fara basu abincin.
Masu zanga-zangar dai sun dage sai an sako shugabansu Ibrahim El-zakzaky da ke tsare biyo bayan arangamar almajiransa da sojoji a birnin Zariya cikin shekarar 2015.
‘Yan kungiyar dai sun bayyana a Abuja ta bangaren kasuwar Wuse, da ci gaba da muzaharar. Jami’in labaran kungiyar na Abuja Saminu Azare, ya ce an sake kama mutane 20 kuma an kai wanda yaji rauni a ka asibiti.
A cewar mai sharshi kan al’amuran yau da kullum Yusuf Isihak Baje, faifan bidiyon da aka watsa dake nuna abin da wasu daga cikin masu zanga-zangar suka yi na daukar makamai suna jifan jami’an tsaro, dole ne ‘yan sanda su dauki matakin kare kansu.
Sai dai jami’in labaran kungiyar Saminu Azare ya nuna jajircewarsu da cewa ba zasu yi ‘kasa a gwaba ba wajen fitowa da nunawa duniya irin zaluncin da ake musu.
Domin karin bayani saurari rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya.
Facebook Forum