Rundunar ‘yan sandan jihar Borno tana neman wani dan siyasa ruwa a jallo sakamakon kashe wani matashi dan shekaru 20 a gidansa.
Kwamishanan ‘yan sandan jihar Daniel Chukwu yace dan siyasan mai suna Grema Teirab ya aika masa wasikar neman izinin yin taro a gidansa. Wasikar na dauke da tambarin jam’iyyar PDP dauke da sa hannunsa. Ya shaidawa Kwamishanan cewa taron na ‘yanuwa ne kawai, ba na siyasa ba ne.
Amma a cewar kwamishanan idan taron siyasa za’a yi bai kamata a yi a gidan shi Grema ba. Kamata ya yi su je irin wuraren da ake gudanar da tarurrukan siyasa. Duk da wannan shawarar da aka bashi, Greman ya gudanar da taron cikin gidansa.
Yayinda ake gudanar da taron ne aka daba ma saurayin, mai suna Maina Mustapha wuka lamarin da ya yi sanadiyar mutuwarsa.
Kwamishanan y ace bayan taron ne ya samu labarin cewa an soki wani da wuka. Jami’ansa sun isa wurin sun tabbatar da hakan ya faru. Sun samu Maina Mustapha cikin jininsa amma wanda ya shirya taron Grema Teirab ya yi ta kare. Sai dai ‘yan sandan sun cafke mutane 24 da suka tarar a gidan. Yanzu dai suna neman mai gidan.
Haka kuma ‘yan sandan sun bukaci Grema Teirab ya fito daga inda ya buya domin shari’a ta yi aikinta. Kwamishanan ya kara da cewa sun samu labara shi Greman ya yi wasu maganganu na harzuka jama’a domin su yi tashin hankali
Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani
Facebook Forum