Alhaji Sani, wanda har wayau shine sarkin samarin Sarkin Daura, yace bukatar samun zaman lafiya da kuma yanayin halin tsaro da kasar take ciki, shi yasa suka kira wannan taro.
Alhaji Sani Iro yace, zasu gudanar da shawarwari kan bukatar samun zaman lafiya, da nufin hana matasa shiga ta'adanci. Shugaban samarin yace akwai bukatar tabbatar da cewa matasa su kasance masu natsuwa, da tarbiya, masu ayyukan yi, da kuma neman ilmi.
A nasa bangaren, Sarkin Samarin masarautar Kano Mallam Ado Sani Mohammed, yace akwai bukatar bangaren matasan da kuma su manya duka su kasance masu hakuri.
Mallam Ado yace, domin a yanzu haka, ko wani bangare yana iya baiwa al'amarin wata irin fasssara.
Ga karin bayani.