Amurka ta fito da babbar murya tana yin Allah wadarai da da mummunan harin da aka kai a kan masu ibada a Babban Masallacin Jumma'a na Kano tare da hare-haren da aka kai cikin 'yan kwanakin nan a kan fararen hula a yankin arewa maso gabashin Najeriya.
A cikin wata sanarwar da ta bayar, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Amurka, Jen Psaki, ta ce Amurka tana nan daram a bayan al'ummar Najeriya a gwagwarmayar da suke yi da tsagera da kuma barazanar ta'addanci.
Ta sake jaddada kudurin Amurka na yin aiki tare da dukkan al'ummar Najeriya wajen takalar irin wadannan ayyuka na rashin imani.
Shi ma babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon, yayi Allah wadarai da wannan mummunan harin da aka kai a kan Babban Masallacin Jumma'a na Kano.
Mr. Ban yace babu wata hujja da za a iya gabatarwa ta kai hari a kan fararen hula, yana mai yin kira ga hukumomi da su gaggauta hukumta wadanda suka aikata wannan ta'addancin.
Shi ma babban sakataren ya sake jaddada cikakken goyon majalisar ga kokarin Najeriya na yakar ta'addanci tare da samar da tsaro ga al'umma ta hanyar bin dokoki na kasa da kasa da kuma ganin cewa Najeriya tana cika hakkinta na kare hakkin jama'a a wajen yakar ta'addancin.