Yawancin mutanen da aka zanta dasu a birnin Kwanni sun yi fatan kasar ta samu zaman lafiya kamar yadda suka gudanar da zabuka ba tare da tashin hankali ba ko wata hatsaniya.
Abu na biyu da dukansu suka yi kira a kai shi ne kowa Allah ya ba idan an bada sakamakon zaben jama'a su karba hannu biyu su yiwa shugaban biyayya. Kada su tada hankali akan sakamako domin Allah ne yake bada shugabanci.
To saidai akwai korafi da wani Alhaji Sani ya yi. Yace kodayake an gudanar da zabe lami lafiya wani abu ya faru da basu taba ganin irinsa ba. 'Yan siyasa suna sayen mutane tamkar bisashe. Idan dan siyasa ya saye mutane ke nan ba zai yiwa ja'ma'a aiki ba. Knasa zai yiwa. Ba zai yiwa jama'a adalci ba domin ya sayesu ne.
Suna dakon sakamakon zabe da fatan za'a tabbatar masu da abun da suka zaba ba tare da karkata kuri'u ba.
Ga karin bayani.