Kimanin ‘yan kasar Nijar dubu biyu ne dai suka yin rajista zaben jamhuriyar Nijar a birnin Lagos, kuma tun da sanyin safiya ne masu neman kada kuri’un suka yi dafifi a cibiyoyin zabe biyar da aka ware domin wannan zabe.
Masu kada kuri’un da dama sun nuna gamsuwar su akan yadda aka tafiyarda zaben.
Shima tunda farko Alhaji Ibrahi,m Usman babban jami’in zaben daya gudana a birnin Lagos yace babu wani cikas koma yana tafiya yadda ya kamata.
An dai gudanar da zaben na birnin Lagos cikin kwanciyar hankali da lumana kuma tuni akakamala zaben na birnin Lagos.