Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An kulla yarjejeniya da shugabanin juyin mulkin kasar Mali



Wasu 'yan kasar Mali suke zanga zangar nuna rashin amincewa juyin mulkin da suja suka yi.
Wasu 'yan kasar Mali suke zanga zangar nuna rashin amincewa juyin mulkin da suja suka yi.

Shugabanin juyin mulkin kasar Mali sun cimma yarjejeniyar da kungiyar habaka tattalin arzikin Afrika ta yamma ECOWAS mai wakilai kasashe goma sha biyar na maida mulki hannun farar hula a kasar ta Mali da yaki ya daidaita.

Shugabanin juyin mulkin kasar Mali sun cimma yarjejeniyar da kungiyar habaka tattalin arzikin Afrika ta yamma ECOWAS mai wakilai kasashe goma sha biyar na maida mulki hannun farar hula a kasar ta Mali da yaki ya daidaita.

An bada sanarwar wannan yarjejeniya ce a gidan talibijin na kasar. An bada sanarwar cewa shugabanin mulkin soja sun yarda a kafa gwamnatin wuci gadi karkashin jagorancin Prime Minista, domin rama wa kura aniyarta kuma, za’a yiwa shugabanin juyin mulkin ahuwa kuma kungiyar ECOWAS zata dage takunkunmin data azawa Mali.. Shugaban Majalisar dokokin kasar shine zai rike mukamin shugaban kasa na wuci gadi domin ya shirya yin zabe.

Kasashen Afrika ta yamma sun baiyana goyon bayansu ga yunkurin da Mali keyi na sake kwato biranen arewacin kasar, wadanda suke hannun yan tawaye Azbinawa. Yan tawaye Azbinawa tare da taimakon mayakan wata kungiyar Musulmi sun mamaye muhimman birane a arewacin kasar kuma a jiya juma’a suka ayyancin yancin cin gashin kan kasar Azawad.

Nan da nan kungiyar kasashen Afrika tayi watsi da wannan ayyana kan cewa bata da ma’ana ko miskalzaratan, haka itama kasar Faransa wadda ta taba yiwa Mali mulkin mallaka itama tayi watsi da wannan ayanawa.

Shugaban jamhuriyar Niger Mahammadou Yusuf ya fadawa sashen Faransanci na Muryar Amirka cewa Mali kasa daya ce wadda ba za’a raba ba.

Jiya juma’a kungiyar ECOWAS tace tana shirye shiryen tura sojoji dubu uku da zasu an kokarin ganin an maido da amfani da dokar tsarin mulkin kasar da kuma jawa yan tawaye burki.

Kasar Faransa kuma, tayi tayin bada taimakon kayayyakin aiki, ciki harda motoci. Jiya juma’a Ministan tsaron Faransa Gerard Longuet yayi wannan alkawari, kuma yayi kira ga kungiyar ECOWAS data yi aikin magance rikicin Mali a siyasance na lokaci mai tsawo inda aka yi shekara da shekaru yan tawaje Buzaye suna fafatawa domin samun ‘yancin cin gashin kai.

XS
SM
MD
LG