Shugaban kasar Venezuela, Nicolas Maduro yace zaben da aka gudanar jiya lahadi na sake rubuta sabon kundin tsarin mulkin kasa ya yi matukar nasara.
Maduro ya shaidawa magoya bayansa a Caracas babban birnin kasar cewa, Mutane “sun tsallaka takuna da tuddai” domin kada kuria’r goyon bayan gudanar da taron shata kundun tsarin mulkin kasa.
Yace " Al’ummar kasar Venezuela sun nuna cewa, idan makomarmu na fuskantar barazana, idan muna fuskantar barazanar rashin kishin kasa, idan muna fuskantar barazanar mulkin mallaka, a lokacin ne muka nuna irin jinin kwatar ‘yanci dake cikin maza da mata da kananan yara da matsa dake."
Hukumar zabe ta kasa tace, sama da mutane miliyan hudu dake wakiltar sama da kashi arba’in da daya cikin dari na wadanda suka cancan kada kuria’ suka gudanar da zabe, duk da zanga zanga da killace hanyoyi da tashin hankali da ya janyo asarar rayukan mutane tara. Yayinda mutane sama da dari da ishirin suka rasa rayukansu a zanga zangar da ake gudanarwa kusan kullum.
Facebook Forum