Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rikicin Venezuela: An Ja Daga Tsakanin Shugaba Maduro Da 'Yan adawa


'Yan adawa sun fake a bayan wani allo yayin da suke artabu da 'yan sanda a lokacin boren nuna adawa da shirin shugaba Nicolas Maduro na kfa wata majalisa a birnin Caracas, ranar 22 ga watan Yuli 2017.
'Yan adawa sun fake a bayan wani allo yayin da suke artabu da 'yan sanda a lokacin boren nuna adawa da shirin shugaba Nicolas Maduro na kfa wata majalisa a birnin Caracas, ranar 22 ga watan Yuli 2017.

An ja daga tsakanin gwamnatin Venezuela da 'yan adawan kasar yayin da ranar da shugaba Nicolas Maduro ya ware domin zaben 'yan majalisa ta musamman da za su sauya kundin tsarin mulkin kasar ke karatowa, matakin da 'yan adawan suka ce ba za ta sabu ba, bindiga a ruwa.

‘Yan adawa a kasar Venezuela sun ba da sanarwar fara zanga-zangar kwanaki biyu a cikin wannan makon domin tursasa wa shugaba Nicholas Maduro ya soke zaben nan da ya kudiri aniyar yi a ranar 30 ga wannan watan domin zaben ‘yan majalisa.

Masu adawar sun "muna kira ga daukacin jama’ar kasa, da kungiyoyi da su shiga cikin yajin aiki na sa’o’i 48 a ranar laraba da alhamis," kamar yadda dan majalisar dokokin Simon Calzadilla ke cewa.

Calzadilla ya ce zanga-zanga za ta biyo bayan yajin aikin a ranar juma'a inda za a bukaci Maduro da ya soke wannan batun zaben a hukumance.

Sai dai shugaban ya yi kememe duk da karuwar zanga-zangar da ake samu a kasar dama kiraye-kiraye daga sassan duniya daban-daban kan shawo kan rikicin ta hanyar sasantawa da 'yan adawan.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG