Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Shiga Kwanaki Biyu Da Fara Yajin Aiki A Venezuela


Shugabannin kungiyoyin adawa na kasar Venezuela na zargin shugaba Maduro da niyyar zama shugaban kama-karya idan har aka yi zaben wakilan da zasu rubuta sabon kundin tsarin mulki da ya ke so.

Bangaren ‘yan adawar kasar Venezuela suma za sun bi sahun masu yajin aiki yau Alhamis, rana ta biyu kuma ta karshe da aka kaddamar da yajin aiki a duk fadin kasar da zummar tilastawa shugaba Nicolas Maduro soke zaben dake tafe na wakilan da zasu rubuta sabon kundin tsarin mulkin kasar.

Miliyoyin ma’aikata sun yi zaman su a gida jiya Laraba, hakan ya sa babu motoci sosai akan hanyoyin da manya tituna, kuma an rufe masana’antu dayawa.

Wasu masu zanga-zanga sun sanya shingaye a wasu unguwarni don hana mutane zuwa wurin aiki, abinda ya janyo hargitsi tsakanin su da dakarun tsaro har mutum daya ya rasa ransa.

Shugaba Nicolas Maduro ya shirya cewa a ranar 30 ga watan nan na Yuli ne za a gudanar da zaben wakilan da zasu rubuta kundin tsarin mulki don maido da doka da oda a kasar Venezuela, bayan da mutane fiye da 100 suka rasa rayukansu a cikin tashe-tashen hankullan da suka rinka barkewa kusan kowacce rana ta Allah tsakanin masu zanga-zanga da jami’an tsaro tun daga watan Afirilu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG