Malaman addinan biyu sun kira 'yan siyasa da shugabanni su tabbatar an dauki matakan ganin an gudanar da zabukan gamagari da kasar zata yi cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya.
Malam Salisu na Malam Atta na kwanar mutuwa cewa ya yi da zara an yi zabe to a tabbatar an ba nasara ga duk wanda Allah ya ba galaba,kada a sauya sakamako. Shugabanni su kiyaye adalci domin shi ne zai tabbatar da zaman lafiya. A ja kunnuwan wadanda zasu gudanar zabe su yi adalci.
Shi ma limamin babban cocin asembli Aliyu Yari kira yayi a tabbatar an yi zabe cikin kwanciyar hankali da tsanaki. Fatansu shi ne a fara zabukan lafiya a kuma kare lafiya. Duk wanda Allah ya ba a bashi kuma Allah ya tayashi rikon amana. Wadanda suka rasa kuma Allah ya basu ikon rungumar kaddara. Su kasance cikin hakuri a yi tafiya dasu.
Kamar malaman addinin musulunci su ma na kirista zasu cigaba da tallafawa wurin yin addu'o'i. Wadanda Allah zai zaba ya basu ikon yin adalci saboda salama ta tabbata a cikin kasar.
Ga rahoton Haruna Mamman Bako.